Tsokaci kan littafin “Gwarzon Afirka Kuma Masaninta: Shehu Usman Danfodiyo” na Ali bin Ghanem…
A yayin da ake ci gaba da bukatar fahimtar tarihin Addini da al’adun Yammacin Afirka, musamman daga ciki da wajen yankin, Ali bin Ghanem…
Tsokaci kan littafin “Gwarzon Afirka Kuma Masaninta: Shehu Usman Danfodiyo” na Ali bin Ghanem Al-Hajri

Book Cover: Gwarzon Afirka Kuma Masaninta: Shehu Usman Danfodiyo (Hausa Translation)
A yayin da ake ci gaba da bukatar fahimtar tarihin Addini da al’adun Yammacin Afirka, musamman daga ciki da wajen yankin, Ali bin Ghanem Al-Hajri ya datse tsawon dubban kilomitoci domin cike wannan gibi a cikin littafinsa mai suna “Gwarzon Afirka Kuma Masaninta: Shehu Usman Xanfodiyo” wanda ya rubuta a kan fitaccen malamin Musulunci a yammacin Afirka, wato Xanfodiyo.
Wannan maqala ta yi nuni da irin rawar da Danfodiyo ya taka a fagen siyasa, gudanarwa, kudi, soji, da kuma fagen addini kamar yadda marubuci dan kasar Qatar Ali Al-Hajri ya nuna. Manufar ita ce amfanuwa da masu karatu da daqunan karatu na Larabawa da na duniya baki daya da wani mutumi da ya yi tasiri mai girma a nahiyar Afirka, musamman a yammacin nahiyar.
A cikin littafin, Al-Hajri ya zayyana tarihin Danfodiyo da yadda yayi tasiri a kan dukkan bangarori da suka shafi siyasa, gudanarwa, kudi, soja, kimiyya da addini na zamanin da lokutan da suka biyo baya. Wannan wani abu ne da ba kasafai ake samunsa ba a cikin dukkan littafai da nassoshi da suka yi bayani kan wannan zamani, domin mafi yawan littafai da ake samu a fagen ilimi kawai suna gabatar da wani bangare na musamman ne ba tare da la’akari da sauran bangarorin ba. Wannan na daya daga cikin dalilan da suka sanya littafin Ali Ghanem ya zama babban abin magana kan rayuwar Shehu Danfodiyo da nasarorin da ya samu a rayuwarsa.
Wannan littafi ya qara samun muhimmanci domin yana daga cikin littafan da suka yi bayani dalla-dalla kan rayuwar Shehun a matsayin wanda ya kafa daula da aka ganin shine irinsa na farko a tarihin Musulunci na yammacin Afirka (1219–1321 AH/1804–1903 AD), wanda ya taso daga yammacin Nijar a yamma zuwa kan iyakokin Borno da ke gabas, da kuma kudu da Sahara. ‘Ya’yansa da almajiransa sun yi mulki tsawon karni guda, har zuwa faxuwar Daular a hannun turawan Ingila a karni na ashirin.
Dangane da abin da littafin ya kunsa, marubucin ya raba shi zuwa babi hudu. Babi na farko ya kawo cikakken tarihin Shehu Danfodiyo, wanda ya fara da asalinsa da haihuwarsa da tarbiyyarsa, ya koma ga matansa da ‘ya’yansa, da siffofinsa har zuwa mutuwarsa, tare da kammala rayuwarsa da aqidarsa na addini, da kuma maganganun wasu malamai game da shi.
Babi na biyu ya tattauna ne kan yunkurin Shehu Danfodiyo na kawo sauyi da matakan da ya bi, musamman wayar da kan al’umma wajen yada saqonsa, da mu’amalarsa da sarakuna, da kafa qungiyar, da faxan da yayi tsakaninsa da masarautun qasar Hausa, da kuma yadda da’awarsa ta ci gaba da yaduwa. A babi na uku na littafin, Dr. Ali bin Ghanem Al-Hajri ya yi nazari kan gagarumin kokarin da Shehu Usmanu Danfodiyo ya yi wajen samar da tsarin gudanar da mulki, yana mai nuni da tsarin halifanci da abubuwan da ke tattare da shi, da suka hada da ka’idar shura, tushen tsarin gwamnati, ma’aikatu, da kuma masarautu. Ya kuma tabo tsarin gudanar da mulki da ya hada da raba kasar zuwa jihohi da yankuna.
Al-Hajri ya kuma tabo tsarin kudi da Shehu Danfodiyo ya kafa kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada, wanda ya kunshi tattalin albarkatun kasa da abubuwan da ake kashewa. Ya kuma tattauna kan tsarin shari’a da suka hada da bangaren sulhu, da tantance korafe-korafe, da hukumar Hisbah. Dakta Ali bin Ghanem Al-Hajri ya kammala wannan babi mai ban sha’awa kuma mai matukar muhimmanci inda ya yi nazari a kan tsarin soja da tsaro musamman sojoji da shugabanninsu da sassansu daban-daban da kuma ‘yan sanda da ayyukansu.
A babi na hudu kuma na karshe, ya yi tsokaci kan kokarin Shehu Danfodiyo, musamman rawar da ya taka wajen bunkasa al’adun Musulunci, da kuma ilimi, koyarwa da yada harshen larabci, da ilmantar da mata. Ya kuma bayyana gagarumar gudunmawa da nasarorin da ya samu wajen rubuta fagagen ilimi da kimiyya daban-daban.
A ƙarshe, wannan ɗan taƙaitaccen zagaya da aka yi na littafin “Gwarzon Afirka Kuma Masaninta: Shehu Usman Danfodiyo” ta bayyana cewa Ali bin Ghanem Al-Hajri ya yi ƙoƙari sosai wajen tsara wannan littafi, tare da bayar da bayanai masu ƙima da cikakkun bayanai game da halayen Shehu Danfodiyo. Ya kuma nuna hazaka wajen ba da labarin nasarorin da ya samu a kowane mataki, musamman na siyasa, addini, gudanarwa, kudi, soja, da kimiyya. Ba makawa hakan ne ya sanya wannan littafi ya zama mai mahimmanci a game da rayuwar Danfodiyo da kuma zamanin da ya rayu a cikinsa.
Ya kamata a lura da cewa, wannan littafi na daya daga cikin jerin rubuce-rubuce da Dr. Ali bin Ghanem Al-Hajri ya yi, wanda ta hanyar wannan gagarumin aikin bincike da ya yi, ya yi kokarin tono tsagwaron gudummawa da al’adun Musulunci, da kuma bayyana irin rawar da ma’abota wannan al’adar ke takawa wajen gina tunanin dan Adam, tun daga mafi nisa na duniya daga gabas zuwa yamma. Sauran ayyukansa da aka buga a kusan a lokaci xaya da wannan ya mayar da hankali kan Almanzor (Al-hajeb Al-Mansur) kasar Andalus (Spaniya a yau) na karni na 10 wanda a matsayinsa na ma’aikacin Khalifancin Umayyawa na Cordoba kuma na hannun damar Halifa Hisham na biyu, ya mulki yankin Iberia a qarqashin mulkin Musulunci.
Shakka babu, Danfodiyo, ya kawo sauyi ta hanyar sabunta tunani, al’adu, da kawo ci gaba ba kawai a Najeriya ba har ma da yammacin Afirka baki daya, kuma Al-Hajri, a kokarin da ya yi, ya samu nasarar zayyano waxannan ababe a cikin littafinsa da ya zuwa yanzu aka fassara shi zuwa manyan harsunan Afirka, musamman Hausa da Fulatanci.
메타데이터
- post_id
- deff2133f25e
- slug
- karatu-cikin-littafin-gwarzon-afirka-kuma-masaninta-shehu-usman-danfodiyo-na-ali-bin-ghanem-deff2133f25e
- url
- https://medium.com/@reveiwer/karatu-cikin-littafin-gwarzon-afirka-kuma-masaninta-shehu-usman-danfodiyo-na-ali-bin-ghanem-deff2133f25e
- canonical_url
- https://medium.com/@reveiwer/karatu-cikin-littafin-gwarzon-afirka-kuma-masaninta-shehu-usman-danfodiyo-na-ali-bin-ghanem-deff2133f25e
- author_url
- https://medium.com/@reveiwer
- status
- ok
- fetched_at
- 2026-07-20 09:25:17